ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayyana cewa rokoki uku ne a jere suka fara faduwa cikin sansanin da farko, sannan wasu uku sufa fada kusa da barikin.
Labarin ya kara da cewa babu wani rahoton dangane da wadanda suka jikata a wadannan hare-hare a har yanzu.
Sai dai har ya zuwa lokacin bada wannan labarin babu wata kungiya ko wani mutum wanda ya dauki alhakin kai hare-haren.
Wasu majiyoyin sun bayyana cewa rokoki 10 suka fada kan sansanin sojojin na Amurka sannan sun ce wasu sojojn Amurka da wasu ma’aikata irakawa a cikin sansanin sun ji rauni.
Wannan dai shi ne hare-hare na biyu kan sansanin sojojin na Amurka dake Al-Balad a cikin sa’o’ii 24 da su gabata. A ranar Lahadin da ya gabata ma an kaiwa wannan sansanin sojojin na ‘yan mamaya hare-hare.
342/